Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da ceto kawo yanzu sun tabbatar da cewa mutum takwas sun rasa rayukansu, yayi rushewar wani bene mai hawa Uku a kasuwar waya ta Beirut.
Ta cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya aikewa da maneman labarai, yace wani bawan Allah mai suna Aminu Sani ne ya kira su, lokacin da lamarin ya faru.
A cewar sa, wadanda aka samu nasarar cetowa sun hada da matasa masu shekaru tsakanin 16 zuwa 46.
KARANTA ANAN: Akwai Buƙatar Kwankwaso Da Peter Obi Su Dawo PDP Don Nasara a 2023 – Makarfi
Dukkanin su mutum takwas din maza, waɗanda suka hada da Naziru AbdulKadir, Magaji Abubakar, AbdulRauf Muhammad, Minjibir Ibrahim, Ahmad Buhari Haruna, Sadiq Haruna, AbdulRashid Basiru da Danladi Kasan.
Saminu Yusuf Abdullahi yace yanzu haka wadanda iftila’in ya rutsa da su na karbar magani a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
Ya kara da cewa tuni an fara bincike kan musabbabin faduwar ginin, da kuma ci gaba da lalube ko zasu samu karin wasu.
A wani labarin kuma: Osinbajo Ya Tashi Zuwa Amurka, Domin Ganawa Da Kamala Harris, Da Sauransu
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a safiyar ranar Larabar nan ya tafi kasar Amurka domin neman hadin kan duniya da goyon baya ga shirin da Najeriya ta kaddamar da shi a kwanan nan.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ya fitar ta ce Osinbajo zai gana da takwaransa na Amurka, Kamala Harris; Kungiyar Bankin Duniya, da sauran abokan hulda.