By Ishaq Dabai
Wani matashi mai kimanin shekaru 25 ya fada cikin ruwa a garin Saye dake karamar hukumar Bichi inda kuma a sana diyyar fadawar tasa rai yayi halinsa.
Rohotanni sun bayyana cewa matashi mai suna Sani Alassan yaje wanka bakin ruwanne kuma tsautsayi yasa shi shiga cikin ruwan da yayi sana diyyar mutuwar sa.
Sannan bayan fadawar tasane aka kira jami’an hukumar kashe gobara ta jihar kano inda suka kai masa daukin gaggawa dan ceto rayuwar sa, sai bayan ciroshi daga cikin ruwan ne suka tarar baya cikin hayyacin sa daga baya kuma aka tabbatar ya mutu.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar kano Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar hadarin.
Inda yace tuni hukumar kashe gobara ta jihar kano ta mika gawar tasa zuwa ga mahaifin sa Alassan Muhammad dan yi masa zana iza.