- Hukumar NEMA a kokarinta na rage wahalhalun da bala’in ambaliyar ruwa ya shaifar, hukumar ta fara rabon kayan agaji ga magidanta 22,658 a Kano
- An shawarci wadanda suka ci gajiyar kayayyakin da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata domin inganta zamantakewa da tattalin arzikinsu da kuma kaucewa sayar da su
- Kananan hukumomi 22 da ke shiyyar sanatoci uku da ke jihar ne za su ci gajiyar kayayyakin tallafin
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA a kokarinta na rage wahalhalun da bala’in ambaliyar ruwa ya shaifar, hukumar ta fara rabon kayan agaji ga magidanta 22,658 da bala’in ambaliyar ruwa ta shekarar 2022 ya shafa kuma masu rauni a Kano.
Darakta Janar na NEMA, Mista Mustapha Ahmed-Habib ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da rabon kayan tallafin ga wadanda suka ci gajiyar tallafin a Kano, kamar yadda Tribune Online ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Hedikwatar Tsaro Ta Musanta Karbar Bukatar Juyin Mulki
A cewarsa, “Karimcin ya kasance a ƙarƙashin Sashin Gaggawa na Rayuwar Tattalin Arziƙi na Musamman (SNELEI) don gidajen da ambaliyar shekarar 2022 ta shafa da kuma masu rauni a cikin jihar.
Amma Ahmed-Habib ya bayyana cewa manufar
don kawo agaji ga wadanda abin ya shafa, ya kara da cewa kayayyakin abincin da aka raba sun hada da shinkafa, wake, dawa, man girki, gishiri, man tumatur da dunkulen magi.
Ya kuma bayyana cewa kayayyakin da ba na abinci ba sun hada da gidajen sauro, tabarmu, barguna, katify, bokitin robobi, saitin tukwanen girki, kayan bayan gida da murhu.
Ya yi nuni da cewa, sauran kayan aikin rayuwa sun hada da injin keken dinki, kayan aikin noma kamar injin nika, irin masara, irin shinkafa, irin gyada, injinan fanfo ruwa, takin ruwa, masu inganta girman amfanin gona, magungunan kashe kwari, maganin ciyawa da kuma injin feshi.
Alhaji Ahmed-Habib ya shawarci wadanda suka ci gajiyar kayayyakin da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata domin inganta zamantakewa da tattalin arzikinsu da kuma kaucewa sayar da kayayyakin.
“An ba da irin shukar amfanin gona da kayan aikin ne domin mayar da manoman gonakinsu, da zaburar da noma da kuma kiyaye abincinmu na kasa a tsakiyar tabarbarewar tattalin arziki.
Babban daraktan ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima bisa goyon bayan da aka basu wajen aiwatar da shirin.
Ya bayyana cewa “An tantance magidanta 660,884 da aka yi niyya don cin gajiyar wannan sa hannun gwamnatin tarayya a fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja,” in ji Ahmed-Habib.
Da yake nasa jawabin gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir-Yusuf ya yabawa gwamnatin tarayya da hukumar NEMA bisa daukar matakin a kan lokaci.
Kabir-Yusuf, wanda mataimakinsa, Aminu Abdulsalam-Gwarzo ya wakilta, ya ce kananan hukumomi 22 da ke shiyyar sanatoci uku da ke jihar ne za su ci gajiyar kayayyakin tallafin.
“Magidanta 979 kowanne daga kananan hukumomi 20 za su amfana, yayin da karamar hukumar birnin Kano da karamar hukumar Tarauni aka rabawa gidaje 1,520 bi da bi.
Alhaji Yusuf yayin da ya bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da kayayyakin cikin adalci, ya sanar da su kudirin gwamnati na tallafawa duk wasu shirye-shirye da za a yi amfani da su wajen rage wahalhalun zamantakewar al’umma da mazauna yankin mu,” inji shi.
Da yake jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Malam Ibrahim Muhammad ya yabawa hukumar bisa wannan karamci, sannan ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su yi koyi da irin nagartar gwamnati na taimakawa mabukata.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kano Ta Sake Bude Asibitin Yara Da Ganduje Ya Rufe
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sake bude babban asibitin kananan yara na Hasiya Bayero da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta rufe.
Wannan ci gaban ya zo ne bayan shekaru 33 da bude shi kuma yana nuna aikin farko da Gwamna ya kaddamar a cikin kwanaki 100 da shiga ofis.