- Dan wasan gaba na Paris Saint-Germain Kylian Mbappe yana tattaunawa da kungiyar don sanya hannu kan sabon kwantaragi
- Wannan dai na zuwa ne bayan da zakarun gasar Ligue 1 ta mayar da dan wasan a cikin tawagar farko
- Hakan ya biyo bayan da Mbappe ya nuna ba zai rattaba hannu kan kwantiragin
Dan wasan gaba na Paris Saint-Germain Kylian Mbappe yana tattaunawa da kungiyar don sanya hannu kan sabon kwantaragi, in ji Foot Mercato.
Wannan na zuwa ne bayan da zakarun gasar Ligue 1 ta mayar da dan wasan mai shekaru 24 a cikin tawagar farko.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: PSG Ta Sanya Dan Wasa Mbappe A Kasuwa
An kora Mbappe zuwa wurin ajiya bayan da ya nuna ba zai rattaba hannu kan kwantiragin da PSG ba.
A wata ganawa da aka yi ranar Lahadi, shugaban kulob din Nasser Al Khelaifi ya shaida wa ‘yan wasan cewa “Kylian na zuba jari a kulob din” kuma a yanzu yana hannun koci Luis Enrique.
Mbappe yanzu ya shiga tattaunawa kan sabunta kwantiragi.
Koyaya, zai zama tsawaita kwantiragin na shekara ɗaya kawai, ma’ana Mbappe zai ɗaure har zuwa shekarar 2025 tare da Les Parisiens.
Dukkan bangarorin biyu kuma suna iya cimma yarjejeniya ta sirri kan batun tashi. Dan wasan mai zura kwallo a raga zai bar babban birnin Faransa a bazara mai zuwa, mai yiwuwa zuwa Real Madrid, yayin da ya mika wa PSG kudin siyan kaya mai tsoka.
A wani labarin kuma, PSG Na Shirin Siyar Da Mbappe Ga Manchester United
Paris Saint-Germain a shirye take ta siyar da Kylian Mbappe zuwa ga Manchester United a wannan bazarar idan har fatan da suke da shi kan Sheikh Jassim mai goyon bayan Qatar ya samu kaiwa Wani matsayi a Old Trafford.
Mbappe ya bayyana karara cewa ba zai rattaba hannu kan kwantiragin shekara daya a kwantiraginsa na PSG ba.
Hakan na nufin cewa yarjejeniyarsa a yanzu da zakarun Ligue 1 za ta kare nan da watanni 12.
PSG ba ta son dan wasan mai shekara 24 ya tafi ba tare da Wani kudi ba, kuma a shirye suke domin biya ln kudin sayan dan wasan gaba a wannan bazarar.
A cewar El Pais, mallakin QSI na kulob din Faransa na shirin sayar da Mbappe ga United maimakon Real Madrid, saboda sun gwammace su yi hulda da Sheikh Jassim, idan yunkurin sa na karbar ya yi nasara.