By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama akalla mutane 59 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da kuma dillalan kwayoyi a lokacin da aka kammala bukukuwan sallar Mauludi, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano, Haruna Kiyawa, yace an kama mutane 35 da ake zargi da aikata fashi da makami, yayin da sauran 24 aka kama da laifukan da suka shafi muggan kwayoyi, ya kara da cewa wadanda ake zargin dukkansu mazauna cikin babban birnin Kano ne.
Kazalika jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa rundunar ‘yan sandan ta kwato makamai da kayan maye daban-daban daga hannun wadanda ake zargin, inda ta gargadi ‘yan iska da dillalan miyagun kwayoyi dasu tuba ko kuma a kama su a gurfanar da su a gaban kuliya, inda ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.
Sannan Kiyawa ya godewa al’ummar jihar bisa goyon baya da hadin kai da suke bayarwa wajen ganin jihar ta zauna lafiya.baya da haka yi kira ga jama’a da su ci gaba da kai rahoton duk wani mutum da suke zargi ko wani abu da suke da alaka da masu laifi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa, su daina daukar doka a hannunsu, yana mai ba da tabbacin ‘yan sandan za su ci gaba da sintiri da kai farmaki a maboyar ’yan ta’adda da bakar fata domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu. dukiya.
Haruna-Kiyawa ya bayyana cewa idan bukatar gaggawa ta taso, za a iya tuntubar su ta wadannan lambobi 08032419754, 08123821575, 08076091271, ko kuma a ziyarci shafin su na “NPF Rescue Me” dake kan manhajar “Play Store”.