Shirin bunkasa noma da kiwo na jihar Kano, KSADP tare da tallafin bankin raya kasa na Musulunci da asusun tallafawa al’umma LLF, sun gudanar da horar da ma’aikatan kiwon lafiya na dabbobi 220, wanda shirin ya tsunduma a cikin ayyukan kiwon lafiyar dabbobi a fadin jihar.
A lokacin da aka fara horon wanda aka gudanar tare da hadin gwiwar Smartex Global Resources Ltd, kwararre a fannin kiwon lafiya, Dokta Garba Saleh, ya bayyana cewa horon na da nufin baiwa sabbin Ma’aikatan Lafiyar Dabbobin Al’umma dabarun kiwon lafiyar dabbobin daidai da ingantattun hanyoyin duniya.
“Sakamakon da ake sa ran matasan zasu samu daga horon sun hada da inganta lafiyar dabbobi da kuma kara yawan kayayyakin da ake noman dabbobi, da karuwar samar da kudin shiga daga dabbobi, da samar da ingantacciyar hanyar shiga kasuwanni da kuma samar da zaman lafiya ga makiyaya da mazauna karkara”.
A nasa jawabin babban Jami’in gudanar da da shirin na jiha Malam Ibrahim Garba Muhammad ya ce sun dukufa wajen ganin an samar da ayyukan kiwon lafiyar dabbobi ga daukacin al’umma, tunda ingantacciyar hanyar fadada ayyukan na bukatar sa hannun bangarori masu zaman kansu.
Ya bayyana cewa, ana kuma sa ran za su hada masu kiwo da hidimar kiwon dabbobi, su hada makiyaya da cibiyoyin kiwon dabbobi kamar yadda kwararru za su rika ba su shawarwari da jagoranci, wanda ma’aikatar noma ta jiha za ta dauki ma’aikata.
A nasa jawabin babban sakataren ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta jihar Kano, Alhaji Balarabe Hassan Karaye ya jaddada cewa likitocin dabbobi ne za su kula da wadanda aka horas da su kuma za su taimaka wajen gudanar da aikin rigakafin dabbobi lokaci-lokaci.
Domin tabbatar da ingancin ayyukansu, ya sanar da cewa KSADP za ta yi musu rajista da hukumar kula da lafiyar dabbobi ta Najeriya domin ba su damar samun lasisin sana’a.
Mahalarta horon sun kasance sun samu tagomashi, baya ga tallafin kayan aikin kowanne, wanda ke dauke da kayan kariya, akwatunan kayan aiki, akwatunan sanyi, magunguna iri-iri.