Kungiyar Kwadago reshen Kano ta bukaci gwamnatin Jihar da ta samar da wasu hanyoyin tattara kudi wadanda zasu dinga samar da kudin da zata dinga amfani da su wajen biyan Ma’aikata albashi da kuma yan Fansho.
Shugaban Kungiyar Kwadagon na Kano Kwamared Kabiru Ado Munjibir ne ya bukaci hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa, wadda ya aikowa da Dimokuraɗiyya, da safiyar yau Alhamis.
Kwamared Munjibir ya kuma baiwa daukacin ma’aikata bisa yadda suka gudanar da bukukuwan sallah Ƙarama cikin halin kunci, sakamakon yadda suka gaza samun albashin su na watan Afrilu.
”Muna sane da irin kukan da ma’aikata ke yi kan rashin samun albashinsu, kuma kuyi hakuri zamu ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin kowa ya samu nasa albashin,” Inji Kwamared Munjibir.
Ya kara da cewa a bangaren su na wakilan ma’aikata, sunyi duk mai yiwuwa wajen ganin gwamnati ta biya Albashin, amma rashin samun kason ta daga gwamnatin tarayya ya tilasta samun jinkirin biyan albashin.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa ma’aikata da dama a jihar Kano suna ci gaba da kokawa kan halin da suke ciki, sakamakon yadda rashin kuɗi ke addabar su.