Gwamnatin jihar Kano ta amince da fitar da naira miliyan 12.5 domin gyara da gyaran motocin bas din Dalibai mata.
Amincewar ta biyo bayan mikawa bukatar hakan ga Majalisar zartarwar ta Jihar Wanda kwamishinan ilimi na jihar Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru ya dauki nauyin gabatarwa.
Da yake bayyana hakan, kwamishinan ya ce gyare-gyaren da za a yiwa motocin bas din, wani bangare ne na nufin kara bunkasa bukatun ‘ya’ya mata zuwa makarantunsu da ke fadin manyan biranen jihar.
A cewar sa wannan karimcin na daga cikin alkawuran da Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dauka na tallafawa ilimin yara mata a jihar.
Sai dai ya bukaci direbobin motocin bas din da daliban da su yi amfani da wannan damar ta yadda na gaba za su amfana.
Kwamishinan ya kuma jaddada aniyarsa ta ci gaba da yin duk Mai yiwuwa wajen ganin cewa ilimi ya samu ci gaba mai girma a jihar Kano baki daya.