Ko’odinetan kula da lafiya matakin farko na karamar hukumar Bebeji a jihar Kano, Sani Umar, ya ce karamar hukumar za ta tabbatar da daukar matakan yaki da cutar Polio da ke yaduwa a yankin.
Umar ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata a yayin taron bitar masu ruwa da tsaki kan yaki da cutar shan inna a yankin.
Ya ce: “Mun yi iya bakin kokarinmu don ganin cewa babu wani yaro da aka bari ba a yi masa allurar rigakafi a kowane zagaye na rigakafin cutar shan inna ba, ganin yadda kwayar cutar da ke dada yaduwa.”
A cewarsa, mayar da martani ga barkewar cutar zai tabbatar da cewa an kare dukkan yaran ta hanyar rigakafi.
A wani labarin Kuma na daban.
Kwastam ta kama Busasshen kifi da Buhunhunan Tabar Wiwi a Iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin
Hukumar kwastam ta Najeriya (NCS), shiyyar jihohin Oyo da Osun a ranar Talata, ta kama wasu masu fasa kwauri 19 tare da kama wasu kayayyaki a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.
Kayayyakin da aka kama sun hada da busasshen kifi, gumammiyar shinkafa, man fetur da kuma tanka.
Sauran sun hada da kunshin kayan sawa da takalma, motoci 17, tayoyin da aka yi amfani da su, buhunan tabar wiwi da kwalayen maganin kwari.
Da yake gabatar da kayayyakin da aka kama a hedikwatar hukumar a jiya laraba, Kwanturola, Mista Adamu Abdulkadir, ya ce rundunar ta tara sama da Naira Billiyan 80 ga gwamnatin tarayya tsakanin watan Nuwamban Shekarar 2021 zuwa watan Janairu, shekarar 2022.
Ya ce, “A tsawon lokacin, rundunar ta kama haramtattun Kayayyaki 356, tsare 46 da kuma kwace 19.”