Wasu ‘yan bindiga da suka Kai hari kan babura bayan a unguwar Adagba da ke karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja, sun yi watsi da babura 10 daga cikin 36 da suka sace yayin da suka kawo harin.
An ce man fetur ya kare a unguwar Zago da ke makwabtaka da jihar Neja.
City & Crime ta ruwaito cewa ‘yan bindigar, a daren ranar Asabar da ta gabata, sun kai farmaki garin Adagba, inda suka kashe mutum daya, suka yi awon gaba da wasu guda takwas, tare da yin awon gaba da babura 36.
Wani mazaunin garin Adagba, Shehu Garba, a lokacin da yake zantawa da wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya a ranar Litinin, ya ce ‘yan bindigar da ke tserewa daga cikin al’umma sun rasa mai a dajin da ke kusa da kauyen Zago, kuma sun yi watsi da babura akalla guda 10 da suka sace a wurin.
Malam Garba ya bayyana cewa, “da misalin karfe 7 na safe (jiya) wani dan kauyen Zago ya bayyana cewa, ‘yan bindigar da suka gudu sun bar babura 10 a cikin daji.”
Madaki na Adagba, Adamu Wambai, ya tabbatar da watsi da baburan da Yan bindigar suka yi, inda ya ce an mayar da su fadar sa.
A wani labarin Kuma na daban.
Kotu ta tura Wani Mutum Gidan yarin Kirikiri kan zargi lalata da Yar Shekara 6
Wata kotun majistare da ke Badagry da ke Legas, a ranar Litinin, ta bayar da umarnin a tsare wani matashi dan shekara 21, Mai suna Tobi David, bisa laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara shida.
Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya, wanda bai amsa rokon David ba, ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan yari na Kirikri sannan kuma ya umurci ‘yan sanda da su aika da takardar karar zuwa ga daraktan karban kararrakin jama’a (DPP) na jihar, domin neman shawara kafin daga bisani a dage shari’ar zuwa watan 6 ga yunin shekarar, 2022.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Nkem Uko, ya shaida wa kotun cewa David ya aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Afrilu da misalin karfe 10 na safe a Ashipa Quarters da ke unguwar Sème a Legas, ta hanyar shigar da yarinyar cikin dakinsa tare da yin lalata da ita.
Mai gabatar da kara ya kara da cewa karamar yarinya tana karbar magani a asibiti. (NAN)