Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun da ‘yan banga da kuma kungiyar tsaro ta Amotekun sun kama wasu mutane tara na wata kungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar hanyar Abeokuta zuwa Ayetoro a karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a jihar.
An kama wadanda ake zargin ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da jami’an tsaro na hadin gwiwa suka kai farmaki maboyarsu da ke Abule Oba da ke kan titin Ayetoro a Abeokuta.
Wadanda ake zargin sun hada da Hammed Taiwo, Kehinde Jimoh, Umar Sanda, Sanda Aliu, Ali Morandu, Usman Abubakar, Usman Mohammed, Umaru Ahmadu da Umaru Momodu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a ranar Litinin, ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan sandan sun tattaro cewa Hammed Taiwo da Kehinde Jimoh, masu sana’ar kabu-kabu da babura ne da ke gudanar da sana’ar yin garkuwa da mutane a boye , an gansu a unguwar Rounder da ke Abeokuta.
Ya ce bayan kammala tattara bayanan sirrin ne ‘yan sandan suka zage damtse inda suka kama mutanen biyu.
Ya ci gaba da cewa, “Da aka yi musu tambayoyi sun amsa cewa suna cikin kungiyar, amma aikin su shi ne lura da muhalli don hana jami’an tsaro kai musu hari yayin da Yan uwansu suka kawo farmaki.
Ya ce wannan ikirari nasu ne ya sa aka gano maboyar ‘yan kungiyar a Abule Oba da ke kan titin Ayetoro, “inda a kullum suke haduwa bayan karbar kudin fansa daga hannun wadanda suka sace.”
Oyeyemi ya ce wasu da abin ya shafa sun bayyana wadanda ake zargin a matsayin wadanda suka sace su.
Awani labari Kuma na daban.
Kotu ta tura Wani Mutum Gidan yarin Kirikiri kan zargi lalata da Yar Shekara 6
Wata kotun majistare da ke Badagry da ke Legas, a ranar Litinin, ta bayar da umarnin a tsare wani matashi dan shekara 21, Mai suna Tobi David, bisa laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara shida.
Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya, wanda bai amsa rokon David ba, ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan yari na Kirikri sannan kuma ya umurci ‘yan sanda da su aika da takardar karar zuwa ga daraktan karban kararrakin jama’a (DPP) na jihar, domin neman shawara kafin daga bisani a dage shari’ar zuwa watan 6 ga yunin shekarar, 2022.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Nkem Uko, ya shaida wa kotun cewa David ya aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Afrilu da misalin karfe 10 na safe a Ashipa Quarters da ke unguwar Sème a Legas, ta hanyar shigar da yarinyar cikin dakinsa tare da yin lalata da ita.
Mai gabatar da kara ya kara da cewa karamar yarinya tana karbar magani a asibiti. (NAN)