An dorawa gwamnatin tarayya alhakin kare ‘yan Najeriya a kasashen waje a matsayin hanyar tabbatar da dorewar ci gaban kasa.
Wasu Kungiyoyin Farar Hula (CSO) sune su kayi wannan kiran, a cikin wata makala mai shafi 10 da aka ba da shawarar dorewar shirye-shiryen hijira daga Najeriya zuwa wasu kasashen ketare a taron kungiyoyin da ya gudana a jiya Jama’a na shekarar 2021, Mai taken: “Human Mobility in the Context of Development”, wanda aka gudanar a Abuja.
Da take gabatar da shawarwarin kungiyoyin CSOs a karshen taron na kwanaki biyu a ranar Juma’a, shugabar kungiyar CSD, Osato Mary Igbinosun, ta ce babu wata tambaya ko ‘yan Najeriya za su iya amfani da ‘yancinsu na yau da kullum.
Igbinosun ya ce, “Don cimma wannan, kare hakkin ‘yan Najeriya a kasashen waje, gina amana tsakanin wadannan kasashen ya zama dole. Ana iya cimma hakan tare da ingantattun ayyukan ofishin jakadancin mu a kasashen waje.”
Don haka ta bukaci gwamnati da ta kuma dauki nauyin ayyukan hijira ta hanyar tabbatar da daukar matakin wajen ware kasafin kudin ga Ma’aikatu, da Hukumomi (MDAs) na gwamnati masu ruwa da tsaki akan lamarin.
Kungiyoyin CSO sun kuma bukaci gwamnati da ta sanya kamfanoni masu zaman kansu a cikin kula da ƙaura tare da haɓaka haɗin gwiwa tsakanin MDAs da CSOs.