Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA za ta fara kame masu tuka babur din Adedeta Sawu da suka ki sabunta takardar izinin tuki.
Manajan Daraktan hukumar, Baffa Babba Dan-Agundi ne, ya bayyana haka a Kano a lokacin da yake zantawa da manema labarai game da ayyukan hukumar a shekarar 2021, ya na Mai cewa, matakin zai zama abin tunatarwa ga matuka Keke Napep da suka kasa sabunta takardar izinin.
“Wadanda zasu samu takardar izinin a karon farko za su biya Naira 18,000, yayin da wadanda za su sabunta ta za su biya N8,000 kacal,” in ji Dan-Agundi, inda ya kara da cewa a hukumance ranar da za a fara kama su I ta ce, a ranar 1 ga Janairu, 2022.
MD din ya kuma ce hukumar ta hada hannu da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) domin kamo direbobin da kuma mika su ga hukumar domin daukar matakin da ya dace.
KARANTA WANNAN LABARIN:Mutane 9 A Kananan Hukumomin 2 Na Jihar Kaduna
Ya ce: “A cikin sabbin tsare-tsarenmu na shekarar 2022, jami’an KAROTA za su fara kame duk direbobin da ba su da mitar kaiyade Gudun Abun Hawa, tare da mika su ga hukumar FRSC.
Dan-Agundi ya kuma ce hukumar ta dauki sabbin ma’aikata 1,000 a shekarar 2021 tare da kara motocin aiki daga uku zuwa 60, da kuma sabbin Mashinan Tsere guda 50.Ya kuma ce a cikin shekarar da ta gabata, jami’an hukumar sun kama barayi wadanda suka yi wa masu amfani da keken Napep wurin satar yara, da kwace wayoyi da sauran laifuffuka kuma yawancinsu an kai su kotu.