Kasar England ta Lallasa Wales da ci 3 da nema a wasan cin kofin duniya na 2022.
Dan wasa Marcus Rashford ne ya fara zura kwallon a minti na 50, da fara wasan.
KU KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnatin Kogi Ta Rattaba Hannu Da Kasar Sin Kan Fasahar Zamani
Daga baya sai dan wasa P. Gordon ya zura kwallon ta biyu a ranar Wales, a mintuna na 51, da fara wasan.
A mintuna na 68 M. Rashford ya sake jefa kwallo ta uku ragar Wales, wanda kuma aka tashi wasan ci 3 da Nema.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a rukunin B. England ce ke jan ragamar teburin da maki 7, sai Wales a karshen teburi da maki daya.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Zamfara Ta Gargadi Jam’iyyar PDP Akan ‘Yan Bangar Siyasa
Gwamnatin jihar Zamfara ta gargadi jam’iyyar hamayya ta PDP da kar ta sa ‘yan bangar siyasa a matsayin dabarun da za ta bi domin ganin ta ci zabe a jihar.
A zantawarsa da manema labarai mataimakin gwamnan jihar, Sanata Mohammed Nasiha, a gidan gwamnatin Gusau, ya zargi jam’iyyar PDP da kuma dan takararta na gwamna da yin amfani da ‘yan barandan siyasa wajen kaddamar da hare-hare kan allunan talla da kadarori na ‘yan jihar da ba su ji ba ba su gani ba.