Gwamnatin jihar Zamfara ta gargadi jam’iyyar hamayya ta PDP da kar ta sa ‘yan bangar siyasa a matsayin dabarun da za ta bi domin ganin ta ci zabe a jihar.
A zantawarsa da manema labarai mataimakin gwamnan jihar, Sanata Mohammed Nasiha, a gidan gwamnatin Gusau, ya zargi jam’iyyar PDP da kuma dan takararta na gwamna da yin amfani da ‘yan barandan siyasa wajen kaddamar da hare-hare kan allunan talla da kadarori na ‘yan jihar da ba su ji ba ba su gani ba.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa aNasiha ya ci gaba da cewa, an sanar da gwamnatin jihar cewa, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Dauda Lawan Dare a ranar 27/11/2022 ya tara ‘yan bangar siyasa tare da lalata allunan talla da dukiyoyin jama’a a Gusau babban birnin jihar.
KU KARANTA KUMA Dan Kwamitin Yakin Neman Zaben PDP, Da Magoya Bayansa Sun Koma Jam’iyyar APC A Zamfara
“Wannan yunkuri ne da PDP da kuma dan takarar gwamna wanda har kotun daukaka kara ta jihar Sokoto ta hana shi shiga harkokin siyasa da suka shafi takarar gwamna.
“Ba za mu bari ’yan siyasa marasa kishin kasa su ci gaba da yin abun da bai kamata ba da za su iya janyowa kokarin Gwamnatin Jiha da Hukumomin tsaro a yakin da ake da kalubalen tsaro da ke addabarsu.
“Zaman lafiya da ake samu a jihar mu har yanzu yana kan tabarbarewar tsaro, don haka ba za mu iya hada hannu don ci gaba da kallon mutanen da ke fakewa da siyasa da nufin mayar da jiharmu a matsayin al’umma marasa bin doka da oda ba“, Nasiha ya yi gargadin.
Jaridar PRIMETIME ta rawaito cewa Ya kuma umurci jami’an tsaro da su tabbatar da kamo duk wadanda suka aikata wannan aika-aika ba tare da la’akari da girman matsayinsu a jihar ba domin doka ta yanke musu hukunci domin hakan zai zama hana wasu.
A Wani Labarin Kuma An Harbe Shugabar Matan Jam’iyyar Labour LP A Jihar Kaduna
An kashe shugabar Matan jam’iyyar Labour Party (LP) a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna, Victoria Chintex har lahira.
Sakataren yada labarai na Jam’iyyar a shiyyar Kudancin Kaduna, Edward Buju, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata.