By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Litinin ne kasar Maroko ta bada umarnin sanarwar dakatar da bukukuwan sabuwar shekara a zaman wani bangare na daukar matakan da zasu dakile karuwar yaduwar cutar Corona.
Gwamnatin kasar ta bada umarnin haramta duk wani nau’in bukukuwa a yammacin jajibirin sabuwar shekara, ciki har da bukukuwa a otal-otal da wuraren yawon bude idanu.
Sannan ta bada umarnin rufe gidajen abinci da wuraren shakatawa da karfe 11.30 na yamma kuma tace za a kafa dokar hana fita daga tsakar dare har zuwa karfe 6:00 na safe a ranar 1 ga Janairu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar 15 ga watan Disamba, kasar Maroko ta gano bullar cutar ta farko na bambance-bambancen Omicron na sabon launin cutar corona.
Bayan wani bangare na sake bude iyakokin, wanda hakan zai sa a sake rufe su daga ranar Alhamis don shawo kan cigaba da yaduwar bambance-bambancen masu kamuwa da cutar.
Sai dai hukumomi za su shirya jiragen na musamman na dawo da ‘yan kasashen waje da suka makale a wasu kasashen.
AFP