By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Litinin din data gabata ya amince da alawus-alawus na albashin wata daya ga masu aikin sa kai dake yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram, wadanda suka hada da jami’an rundunar hadin gwiwa ta farar hula da mafarauta, a matsayin kyauta na karshen shekara.
Gwamnan ya hada da ma’aikatan tsaftar muhalli dake aikin tsaftace al’ummomin da ‘yan tada kayar baya suka lalata kafin a sake gina su da kuma masu tsaftar muhalli dake aiki a cibiyoyin gwamnati da hukumomi da ma’aikatan jinya a wannan mataki.
Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga shugabannin masu aikin sa kai da masu aikin tsafta a Maiduguri, babban birnin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa, wannan garabasar da aka bayar baya ga tallafin da aka samu a baya ta hanyoyi daban-daban, ita ce nuna godiya ga masu aikin sa kai bisa sadaukarwar da suka yi wajen kara taimakawa sojoji da sauran jami’an tsaro a yakin da suke da ‘yan tada kayar baya.
“Dukkanku, ’yan agajin mu, kuna aiki tukuru domin tabbatar da jihar Borno. Duk da cewa kuna cikin dubbai, babu wani tallafi daya yi yawa idan aka yi la’akari da sadaukarwar da kuke yi,” inji shi.
Dangane da ma’aikatan tsaftar, Gwamnan yace “da yawa daga cikin ku kan tashi da karfe shida na safe don tsaftace tituna. Da yawa daga cikinku kuna da hannu wajen tsaftace al’ummominmu kafin sake ginawa.
“Mun gane cewa gudummawar ku na da mahimmanci kuma muna gode muku sosai
Kazalika Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito Zulum ya kuma sanar da sakin buhun shinkafa guda daya ga kowane daya daga cikin masu aikin sa kai da masu aikin tsaftar muhalli a matsayin karin tallafi.