Hukumar kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA) ta ce daga cikin laifukan fyade 5,000 da aka samu a jihar Adamawa a shekarar da ta gabata, kashi 10 ne kawai aka gurfanar da su a gaban kuliya saboda rashin kwararan hujjoji.
Ulla Mueller, Wakilin UNFPA, wanda Chris Sabum, shugaban yankin Arewa maso Gabas ya wakilta, ta bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani kan tantancewa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ma’aikata Sun Bukaci Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda Ya Yi Murabus
Ta ce makasudin taron shi ne karfafa tsarin tabbatar da adalci ta hanyar amfani da tantancewa.
Muller ta bayyana cewa sun kaddamar da wani dakin binciken a asibitin koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama (UMTH), Yola inda za a gudanar da binciken tantance masu laifi a matsayin shaida kan shari’ar da kotu ta yi.
Da yake jawabi a wajen taron, Dokta Kizzle Shako, kwararre kan harkokin shari’a, ya bukaci mahalarta taron da su yaba da rawar da likitocin bincike ko kimiyya ke takawa wajen gudanar da GBV da kuma yadda kwararrun likitocin za su taimaka wa masu binciken su hada karfi da karfe don tabbatar da hukunci da kuma kare al’umma.
Sakatariyar dindindin,a ma’aikatar harkokin mata da ci gaban jama’a, Saso Benson Ali, ta yaba da kokarin da UNFPA da Spotlight Initiative suka yi na dakin gwaje-gwajen bincike inda ta kara da cewa tare da binciken za a kama wasu masu aikata laifuka tare da gurfanar da su a gaban kotu.
A wani labarin kuma, Kaduna: Iyayen Yara Sun Sha Alwashin Ba Za Su Bar ‘Ya’yansu Su Koma Makaranta Ba
Yayin da aka koma makarantun firamare dana sakandare a fadin jihar Kaduna, wasu daga cikin iyaye da dama sun sha alwashin cewa yaran su za su ci gaba da zama a gida idan ba a samar da matakan tsaro ba.
A cikin da’irar da ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna ta fitar mai dauke da sa hannun Adama Yahaya, ta umurci makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da su ci gaba da aiki a ranar Lahadi 4 ga watan Satumba, 2022.