Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya yi karin haske kan yadda gwamnatinsa ta ceto manyan makarantu daga durkushewa saboda rashin tallafi, yana mai cewa gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da makarantun gaba daya.
Wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Rafiu Ajakaye, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar godiya da shugaban kungiyar hadin gwiwar ma’aikatan jami’a a, manyan makarantun jihar Kwara, Bilikis Olasehinde ya kai masa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kashi 10 Ne Kawai Cikin 5,000 Aka Tuhume Su Da Aikata Laifukan Fyade A Adamawa – UNFPA
A cewar AbdulRazaq, gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da makarantun gaba daya; ba su biya albashi ba, balle a gyara ababen more rayuwa.
“Ba su damu da hakan ba. Cibiyar farko da na ziyarta ita ce Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara (Technical) Lafiagi kuma na yi takaici matuka Gwamnatin jihar ta yi watsi da ayyukanta na tsawon shekaru.”
“Mun yi farin cikin biyan bukatunku, Duk da yake za mu yi farin cikin yin ƙarin hakan, yana haskakawa kowa da kowa cewa muna fitowa daga mummunan zamanin da babu wanda ya isa ya sake fata.”
“Gwamnatin da ta gabata ba ta ma iya biyan albashin ma’aikata a lokacin da ake biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 18,000 ba. Yanzu, mun koma biyan Naira 30,000 mafi karancin albashi, mun ma tabbatar da cewa a lokacin da kuke gabatar da bukatunku ana biyan ku albashi.”
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar dawo da martabar jihar Kwara da aka rasa a fannin ilimi tare da zuba jarin da ya dace a bangaren ababen more rayuwa, jin dadin ma’aikata da sauran tsare-tsaren tallafi.
“An kafa jihar Kwara a lokaci guda tare da jihar Legas da wasu. A yau Legas tana da jami’o’in jihohi uku domin sun tafiyar da kansu sosai. Suna kan yanayin sama, mu kuma muna nitsewa kawai. Muna godiya ga Allah da jama’ar da suka ba mu damar dakatar da rugujewar.”
“Mun dakatar da shi kuma muna juya abubuwa zuwa ga kyau. Za mu tabbatar an yi abin da ya dace. Haka kuma tun shigowar mu ba mu kara kudin makaranta ba, mun daskarar da shi wanda hakan na nufin kusan muna ba dalibai rangwame duk da hauhawar farashin kayayyaki. Mun kuma mayar da subvention a kwalejojin mu.”
“Tunda mun sanya al’amurran da suka shafi rage albashin ma’aikata da kuma mafi karancin albashi, mataki na gaba shi ne ganin yadda za mu inganta kayan aiki a cibiyoyinmu. Za mu kuma duba yadda zaku fadada sassan makarantu da kayan aiki, mu hada hannu waje guda mu yi abubuwan da suka dace don ganin ilimin mu ya yi karfi da kuma sanya shi a inda ya kamata.”
“Jihar Kwara ta kasance tana jagorantar ilimi a arewa a da. Mun sauka amma muna kan hanyarmu ta komawa, In Sha Allaahuza mu sake kai wa kololuwa.”
Sai dai malaman sun yabawa gwamnan kan yadda ya ceto manyan makarantun jihar daga durkushewa gaba daya.
Sannan malaman sun bayyana cewa jin dadin su ya samu kyautatuwa a karkashin gwamnan, inda suka ce suna alfahari da matakin da suka dauka na mara masa baya a shekarar 2019.
Olasehinde ya yabawa hukumar bisa aiwatar da tsarin albashin ma’aikatan da aka kafa na Consolidated Polytechnics and Colleges of Education wanda aka shafe shekaru da dama ana yi.
“Mun zo nan ne domin mu nuna godiya ga duk abin da kuka yi mana, mai girma gwamna Lokacin da ka shigo jihar Kwara, akwai batutuwa a manyan makarantun jihar. Mun samu matsalar bashin albashi kuma muna yajin aiki. Nan take kun shigo, muka ce mu dakatar da yajin aikin da kan mu, mu baiwa sabuwar gwamnati shakku. Mun gode wa Allah da ya yi haka domin cikin sa’o’i 24 mun hadu da Gwamna ka yi abin da ka yi alkawari. Muna godiya da hakan,” in ji ta.
A wani labarin kuma, Ma’aikata Sun Bukaci Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda Ya Yi Murabus
Wasu fararen hula na ma’aikatan hukumar ‘yan sanda sun bukaci shugaban hukumar Musilu Smith da ya yi murabus cikin gaggawa saboda yajin aikin da ‘ya’yan kungiyar suka fara shiga mako na biyu.
Ma’aikatan da suke ya yajin aikin, wadanda suka gana a Abuja a karshen mako, sun sha alwashin kada kuri’ar yanke kauna ga kwamitin hukumar karkashin jagorancin Smith, Sufeto Janar na ‘yan sanda mai ritaya, bisa zargin rashin gaskiya.