By Abbas Yakubu Yaura
Kimanin kashi daya cikin hudu na mutanen kasar Somaliya na cikin hadarin fuskantar matsananciyar yunwa sakamakon fari daya addabi kasar sakamakon yakin shekaru da dama, bayan rashin karancin ruwan sama na yanayi uku, in ji majalissar dinkin duniya a ranar Litinin.
Majalisar Dinkin Duniya na fatan rikicin zai kara kamari kuma mutane miliyan 4.6 zasu bukaci agajin abinci nan da watan Mayun sabuwar shekarar 2022, saboda kasar ba ta taba fuskantar rashin damina uku a jere ba cikin sama da shekaru 30.
Karancin abinci, ruwan sama da kiwo tuni ya tilastawa mutane 169,000 barin gidajensu, adadin da zai kai miliyan 1.4 cikin watanni shida, in ji majalisar dinkin duniya a cikin wata sanarwa.A cikin ‘yan shekarun nan, bala’o’i – ba rikice-rikice ba – su ne babban abin dake haifar da kaura a Somaliya, kasar dake cikin wadanda suka fi fuskantar matsalar sauyin yanayi.
Wani babban jami’in kula da ayyukan jin kai na majalisar Dinkin Duniya a Somaliya Adam Abdelmoula, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, bala’i ne da ba a taba ganin irinsa ba, yana mai kiyasin cewa yara 300,000 ‘yan kasa da shekaru biyar na fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki a watanni masu zuwa.
“Zasu mutu idan ba mu taimaka musu nan bada jimawa ba,” in ji shi, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta nemi tallafi dala biliyan 1.5 don tallafawa rikicin.
Kimanin mutane miliyan 7.7, kusan rabin al’ummar Somalia miliyan 15.9, za su bukaci taimakon jin kai da kariya a shekarar 2022, karuwar kashi 30% cikin shekara guda, a cewar MDD.
Akalla kashi bakwai cikin goma na Al’ummar Somaliya suna rayuwa kasa da kangin talauci kuma fari ya lalata hanyoyin samun kudin shiga — asarar dabbobi, raguwar girbi duk hade da hauhawar farashin kayayyaki.
“Hatsarin yana da yawa wanda idan ba tare da taimakon jin kai cikin gaggawa ba, yara, mata da maza zasu fara fuskantar yunwa a Somaliya,” in ji ministar harkokin jin kai da magance rikice-rikice na Somaliya, a cewar Khadija Diriye.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamnatin Somaliya ta ayyana fari a matsayin gaggawar jin kai a watan Nuwamba.
Hakazalika a baya-bayan nan an yi fama da fari da ambaliyar ruwa a kasashen Kenya da Sudan ta Kudu, inda suka kashe dabbobi, da lalata wuraren kiwo da barnata amfanin gona.
Rashin ruwa da abinci ya haifar da fargabar rikici tsakanin al’ummomi kan albarkatun ruwa da sauran su.
Masana sun yi imanin cewa yawaitar da kuma tsananin yanayin na karuwa, suna danganta hakan ga sauyin yanayi.
Comments 1