Adadin kudin da gwamnatin tarayya ke kashewa a matsayin tallafi kan kowace litar man fetur a halin yanzu ya haura N600, kamar yadda masu gudanar da harkokin mai suka bayyana a karshen makon da ya gabata.
Har ila yau, sabbin bayanan da mutanan suka fitar daga kamfanin mai na Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata sun nuna cewa yawan man fetur a kullum a Najeriya ya kai lita miliyan 66.8.
Idan aka yi la’akari da wannan adadi na Hukumar NNPC, hakan na nuni da cewa Gwamnatin Tarayya na kashe kusan Naira Biliyan 40.1 a kullum wajen tallafa wa kowace litar man fetur da ake sha a Najeriya da akalla N600.
Hakan kuma na nufin gwamnati na kashe kusan N1.243tn wajen biyan tallafin man fetur duk wata, kamar yadda ‘Yan kasuwar man sun shaida.
Su kara da cewa, farashin man fetur (idan ba a tallafa masa ba kamar yadda ake yi a Najeriya) sai tsadar sa ta haura n man Dizel.
Sun kara da cewa a halin yanzu farashin dizal yana tsakanin N800 zuwa N850/lita, yayin da kudin tallafin man fetur da aka amince da shi ya kasance a kan N165/lita. Diesel ba a tallafi.
A baya dai wasu masu gudanar da harkokin man fetur sun tabbatar da matsayinsu, ciki har da Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin na NNPC, Mele Kyari.
Hakan na nuni da cewa, a halin yanzu gwamnatin tarayya ta hannun kamfanin mai na kasa NNPC, ba ta kashe kudi kasa da Naira 600 a matsayin tallafi ga kowace litar man fetur da ake sha a fadin kasar nan.
Kamfanin mai na NNPC ya kasance shi kadai ne ke shigo da man fetur a Najeriya tsawon shekaru.