Masu Sana’ar turawa POS, a wasu sassa na jihar Kaduna, sun bar wuraren kasuwancinsu, domin neman wasu hanyoyin da za su cigaba da kasuwanci, biyo bayan rufe hanyoyin sadarwa a sassan jihar.
Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne gwamnatin jihar Kaduna ta rufe hanyoyin sadarwa a kananan hukumomin Brinin Gwari, Chikun da Kajuru, a matsayin wani mataki na magance matsalar rashin tsaro.
Wasu daga cikin ma’aikatan da suka yi magana da Kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN a ranar Talata sun ce ba su da wani zabi da ya wuce su koma wuraren da za su iya shiga yanar gizo don cigaba da aiwatar da kasuwanci.
Sarah Francis, wata mazauniyar Sabo, ta shaida mana cewa duk da ta samu wani shago, ta biya kudin hayar shekara guda, sai ta koma Barnawa domin ta samu damar shiga hanyar sadarwa ta kuma yi aiki daga can.
“Na roki wata kawata da ke da shagon wanke Kai a Barnawa da ta bar Ni na tsuguna a shagonta, Kasuwanci baya tafiya saboda tallatawa ya ragu tunda akwai masu gudanar da POS da yawa a nan,” in ji Francis.
Nduka Chukwuma wanda ke zaune a Mararaban Rido, a nasa bangaren ya ce ya bar harabar kasuwancin sa ne domin ya yi aiki a gefen titin da ke kan titin Gwari.
“Ina kashe kusan Naira 1,000 a kullum wajen kudin mota da cin abinci a nan titin Gwari tun da ba zan iya yin aiki a shagon da na nake da shi kusa da gidana ba da ke Mararaban Rido.
“Na san ƙalubalen hanyar sadarwa na ɗan lokaci ne amma rayuwa ta yi wahala. Don haka ina rokon gwamnati da ta sake tunani kan matsayar ta domin rayuwa ta dan samu sauki ga mutane,” in ji Mista Chukwuma.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito, shima wani mai suna Bulus Ishaku, mazaunin Unguwan Romi, ya ce “Ina zagawa dauke da injina a wuraren shakatawa a kusa da Barnawa, wani lokacin kuma a Kakuri.
“Mai kula sa gida ya zama matalauci saboda abokan ciniki sun fi son masu aiki da ke zama a cikin shagunan su don guje wa matsalar gazawar hanyar sadarwa.
“Hakika, wasu lokuta mutane suna kallon masu amfani da POS ta wayar hannu a matsayin ‘yan damfara, hakan yana shafar masu sana’ar,” in ji Mista Ishaku.
Shi kuma wani mai mu’amala da masu sana’ar ta POS Innocent Bala na Barnawa, ya ce ya daina baiwa ma’aikatan POS tun lokacin da ya sami matsala da hanyar sadarwa bayan ya samu matsala wajen hada-hadar kasuwanci.
“Na aikawa abokina kudi kuma aka aka tura masa amma abin takaici, abokina ba a bashi ba yayin da ma’aikacin ya ce cinikin ya yi nasara har ma ya ba ni shaidar rasit,” in ji Mista Bala.
Comments 1