Tsohon sanata Shehu Sani ya caccaki matakin da aka dauka na katse samar da wutar lantarki ga Nijar, yana mai cewa hakan zai kara sanya ‘yan Nijar su rayu ba tare da dogaro da uwayen gidan waje ba.
Dan majalisar a ranar Juma’a ya bayyana rashin jin dadinsa a kan katse wutar lantarki ga Nijar.
Rahotanni sun ce Najeriya ta katse wutar lantarki ga Jamhuriyar Nijar a matsayin daya daga cikin takunkumin da kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta kakaba mata kan juyin mulkin da aka yi a kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa, ana samun yawaitar wutar lantarki a Nijar fiye da yadda ake yi a lokutan baya domin wutar lantarkin ta tsaya tsayin daka kusan awa daya a wani lokaci ga mazauna biranen Yamai, Maradi, da Zinder.
Sani ya yi karin haske kan yadda Najeriya ke dakatar da samar da wutar lantarki ga makwabciyarta ta arewa.
Ya bayyana cewa katse wutar lantarki ga Jamhuriyar Nijar yana shafar asibitocinsu da Makarantu da gidajensu da ofisoshinsu har da fannin kasuwanci su.
KARANTA NANGwamnatin Sojin Burkina Faso ta Dakatar da Wani Gidan Rediyon Kan Sukar Juyin Mulkin Nijar
Wannan ba wai matsin lamba ne ga gwamnatin soja ba, illa azabtar da talakawan kasar da kuma haifar da tsangwama ga kasarmu ta Najeriya daga yan kasar.
Matakin da Najeriya da Ecowas suka dauka yana kara ingiza ‘yan Nijar wajen yin gangamin goyon bayan gwamnatin Soja. Faransa, Ecowas da Najeriya suna tura su don koyon rayuwa ba tare da dogaro da kowa ba
Ya kamta gwamnatin Najeriya da hukumar ECOWAS su gane cewar wannan mataki da suke dauka akan kasar Nijar ba wai yana gyara al’amura bane illa dai yana kara saka
Yam kasar su Tsaki Najeriya da ECOWAS su kuma kara goyon bayan mulkin soji da akeyi kasar dake yammacin Afirika
A WANI LABARIN KUMA
Bazoum Da Iyalinsa Na Cikin Wani Mugun Yanayi-ECOWAS
Hukumar ECOWAS ta bayyana yanayin da hambararren Shugaban kasar Nijar ke ciki a matsayin mummunan inda suka yi kira da a sake shi daga inda yake boye bayan karbar mulki daga hannunsa