- Kotun Majistare dake zamanta a Jos ta yanke wa wani dan kasuwa mai suna Samuel Jigede mai shekaru 35 hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari bisa samunsa da laifin aika sanarwar biyan kudi ta karya wato
- Mai gabatar da kara ya ce mai laifin ya sayi kaya kuma ya aika da alerts na bogi ga masu sayar da kayan kafin a kama shi
- Alkalin kotun ta ce hukuncin zai zama hana wasu masu son aika laifi
Kotun Majistare dake zamanta a Jos a ranar Juma’a ta yanke wa wani dan kasuwa mai suna Samuel Jigede mai shekaru 35 hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari bisa samunsa da laifin aika sanarwar biyan kudi ta karya wato (fake alerts) bayan ya siya kaya.
Mai shari’a Shawomi Bokkos, ta yankewa Jigede hukuncin a takaice bayan ya amsa laifinsa.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta Dakatar da Wani Gidan Rediyon Kan Sukar Juyin Mulkin Nijar
Sai dai Bokkos ta bai wa wanda aka yanke wa hukuncin zabin biyan tara da kuma diyya ta Naira N15,000 domin ya shafe watanni uku a gidan yari.
Alkalin kotun ta ce hukuncin zai zama hana wasu masu son yin laifi, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, Insifekta Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa an kai karar ne a ranar 11 ga watan Yuli a ofishin ‘yan sanda na ‘C’ Division da ke Jos ta hannun wani Uzochukwu Nwakasi, mai shigar da kara.
Mai gabatar da kara ya ce mai laifin ya sayi kaya kuma ya aika da alerts na bogi ga masu sayar da kayan kafin a kama shi.
Laifin dai a cewar mai gabatar da kara, yana da hukunci a karkashin tanadin dokar laifuka ta jihar Filato.
A wani labarin kuma, Miliyoyin Mutane Ne Suke Cikin Yunwa Sakamakon Rikicin Sudan – UN
Yakin da ake gwabzawa a Sudan ya haifar da matsananciyar matsalar yunwa ga mutane miliyan 20.3 a cewar wata sanarwa da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a ranar Juma’ar nan.
Daga cikin mazauna kasar miliyan 46, kimanin mutane miliyan 6.3 ne ke fama da matsalar karancin abinci, in ji Eddie Rowe, wakilin shirin samar da abinci na duniya a Sudan.