Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta gurfanar da wani Sa’adu Maiwada, mataimakin Akanta Janar na Jihar Katsina, tare da Sani Lawal BK a gaban Mai Shari’a M.S Abubakar na Babbar Kotun Tarayya da ke Katsina.
Gurfanar da mutanen biyu ya biyo bayan tuhume-tuhume biyu da ake yi musu na hada baki da kuma karkatar da makudan kudade, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Haɗa Rajistar Masu Jefa Ƙuri’a Ta INEC da NIN Zai Tabbatar Da Sahihancin Zaɓe – Aregbesola
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kuma bayyana cewa ta gurfanar da wani kamfani mai suna Integrated Gas Services Limited a gaban kuliya tare da wadanda ake tuhuma, inda wanda ake kara na farko ya ninka matsayin Manajan Darakta.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na Twitter da aka tabbatar a ranar Talata.
Hukumar EFCC ta yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki ne suka karkatar da makudan kudaden da suka kai N261, 869. 824.00 daga asusun gwamnatin jihar Katsina, a lokacin da suke rike da mukamin karamin ma’aji da mataimakin ma’aji a ofishin Akanta Janar na jihar Katsina a lokacin. .
Hukumar ta yi ikirarin cewa kudaden da aka sace an fitar da su ne ta hannun kamfanin Integrated Gas Services Limited da wanda ake kara na farko (Maiwada) a matsayin darakta.
Sai dai wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da shi, yayin da kotun ta shigar da karar ‘babu laifi’ ga wanda ake kara na uku, Integrated Gas Services Limited.
A halin da ake ciki, Lauyan wadanda ake kara, J.P. Israel, ya mika bukatar neman beli a madadinsu tare da rokon kotu ta bayar da belinsu.
Mai shari’a Abubakar ya bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan tsabar kudi Naira miliyan 50,000,000 kowannensu tare da tsayayyun mutane biyu wadanda dole ne su zama mazauna jihar Katsina.
Alkalin kotun ya kuma bukaci wadanda ake tuhuma da su ajiye fasfo dinsu na kasa da kasa a wurin rajistar kotun sannan daga bisani ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Oktoba.
A wani labarin kuma,Tsohuwar Minista Ta Maida Martani Kan Sabbin Tuhume-Tuhumen da EFCC Ke Mata
Tsohuwar ministar sufurin jiragen sama kuma Sanata, Stella Oduah ta yi fatali da sabbin tuhume-tuhumen da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi mata.
Da take bayyana cewa tuhumar na da nasaba da siyasa da kuma harin siyasa na jinsi, ta ce ba ta da masaniya game da tuhume-tuhumen da “ba su da wata shaida da ke dauke da bayanin nata kamar yadda doka ta tanada.”