Majalisar dokokin jihar Bauchi ta dauki harshen Hausa baya ga turanci wajen gudanar da harkokin majalisar inji jaridar Daily Trust
Kakakin majalisar, Rt Hon Abubakar Y Suleiman ne ya sanar da hakan a zauren majalisar jim kadan bayan dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Shira, Hon. Auwal Hassan, ya gabatar da kudiri, a ranar Talata
Hassan ya ce yaren Ingilishi shi ne yaren da aka amince da shi don gudanar da ayyukan gwamnati da masu zaman kansu a Najeriya
Sashe na 97 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da kuma doka ta 3 da ta 8 na kundin tsarin mulkin jihar Bauchi na 2017
Dokar ta tanadi cewa za a gudanar da shari’o’i da muhawarori na majalisar cikin harshen Ingilishi
KARANTA NANHaɗa Rajistar Masu Jefa Ƙuri’a Ta INEC da NIN Zai Tabbatar Da Sahihancin Zaɓe – Aregbesola
Ya kara da cewa, harshen Hausa da aka fi amfani da shi wajen magana a Bauchi, wanda sama da kashi 90% na al’ummar jihar ke amfani da shi wajen sadarwa,
ya kamata a karbe shi baya ga Ingilishi a matsayin harshen hukuma na biyu
A karo na biyu da kudirin, Hon. Musa Wakili Nakwada mai wakiltar mazabar Bogoro, ya yabawa abokin aikin sa kan wannan kudiri, inda ya tuna cewa shima ya taba gabatar da wannan kudiri a majalisa ta 9
Bayan da shugaban majalisar ya gabatar da kudirin an kada kuri’a, majalisar ta amince da shi inda zaa cigaba da yin ayyukan majalisar da harshen Hausa daga wani sati mai kama wa
A WANI LABARIN KUMA
Da Dumi Dumi Kungiyar PSG Tayi Babban Kamu
Bayan da Hernandez ya lashe gasar lig da kofin gida biyu, Hernandez ya taimaka wa kungiyar Hansi Flick ta doke PSG ta lashe gasar zakarun Turai
Hernandez, wanda ya buga wa zakarun Bundesliga wasanni 107 kuma ya zura kwallaye biyu, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru biyar a PSG