Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Katsina ta bukaci mazauna yankin da su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali domin zaben ‘yan takarar da suke so ba tare da tashin hankali ko tsangwama ba.
Shugaban hukumar, wanda kuma shi ne Grand Khadi na jihar, Dr Muhammad Abubakar, ya yi wannan kiran a ranar Laraba a Katsina a wani taron manema labarai.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Abubakar ya ce a mahangar addinin Musulunci, zabuka da tsarin zabe na nufin a ba ‘yan kasa dama da ba su damar gudanar da ayyukansu na jama’a wajen zaben shugabanni da wakilan da suke so.
KU KARANTA KUMA Miniatan Shari’a Ya Rubutawa Shugaban Kasa Wasika
Ya ce saboda haka su daure su tabbatar sun yi amfani da irin wadannan hakkoki da zabi cikin lumana.
Shugaban ya yi ishara da fadin Allah a cikin Alkur’ani, sura ta 2, aya ta 195: “…. Kuma kada ku jefa kanku da hannuwanku zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; Lallai Allah Yana son masu kyautatawa”.
Ya ci gaba da cewa, Musulunci gaba daya ya yi hannun riga da tashin hankali, zalunci, mugubta, ’yan daba da duk wani aiki da ake da nufin tsoratarwa, muzgunawa ko haddasa fitina ga jama’a.
Abubakar ya kara da cewa, Annabi Muhammad (SAW) ya ce: “Ya ishi musulmi zunubi ya wulakanta dan uwansa musulmi.
“Dukkanin al’amura na zalunci musulmi haramun ne ga dan’uwansa musulmi: jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa“.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa da masu kada kuri’a suna bin Dokokin zabe da tsari da ka’idojin zabe da kuma dokar hana kalubalan tsaro da gwamna ya sanya wa hannu.
A Wani Labarin Kuma Zabe: Atiku Ya Yi Watsi Da Wani Faifan Bidiyo Da Ya Yi Zargin Shirya Magudi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Juma’ar nan ya bayyana wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta a matsayin “shifcin gizo” inda ake zarginsa da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa, da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bayyana shirin yin zagon kasa a zaben da ke tafe.
A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Mista Phrank Shaibu ya fitar a Abuja, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce faifan bidiyon ya tabbatar da cewa jam’iyya mai mulki za ta dauki farfagandarsu zuwa wani sabon matsayi na sa’o’i kadan don kada kuri’a.