Kungiyar Marubuta Harkokin Wasanni Ta Katsina Zata Shirya Gasar Kwallon Kafa Ga Ma’aikatan Shari’a
Kungiyar Marubuta Harkokin Wasanni Ta Kasa Reshen Jihar Katsina (SWAN) zata hada hannu da Babbar Kotun Katsina domin shirya Gasar Kwallon Kafa ga Ma’aikatan Shari’a a Jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Magidanci ya nemi Kotu ta raba Aurenshi da Matar shi, bayan ta Lalata Naira miliyan 2 a Abuja
Babban Jojin Jihar Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacinda ya karbi bakuncin Shuwagabannin Kungiyar Marubuta Wasannin a wata ziyara da suka Kai mashi.
Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ya maganta akan muhimmancin shigar Ma’aikatan Shari’a a Harkokin Wasanni, ya cê yin hakan zai taimaka masu wurin inganta lafiyar jikin su.
Daga nan sai ya tabbatar da cewa a shirye yake ya bayar da goyon bayanda ya dace ga SWAN domin inganta rohotanninsu na harkokin Wasanni.
Tunda farko Shugaban Kungiyar Kwamarad Nasir Sani Gide, yace sun ziyarci Babban Jojin ne domin gabatar da kansu da neman goyon bayanshi ga Kungiyar.
Kwamarad Nasir Sani ya yabawa Babban Jojin akan goyon baya da tallafi da yake baiwa Harkokin Wasannin Guragu da hakan ya taimakawa tawwagar Jihar Katsina ta samu nasara a gasa daban-daban.