By Ishaq Dabai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa hukumar kula da cigaban kasa NALDA, umarnin samar da hade dukkanin kadarorin yankuna dan bunkasa harkar samar da a binci a cikin kasar nan.
Sakataren zartarwa na hukumar Mr Paul Ikonne shine ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar lahadi, yace wannan umarni yazone a yayin gudanar da tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.
A cewar sa shugaban kasa ya kaddamar da irin wannan shirin a Daura dake jihar Katsina, ya kara da cewa NALDA ta fito domin kammala gonakin da suka rage guda 108 bisa umarni na shugaban kasa.
Sannan yace fatan wannan shirin zai taimaka wajen ciyar da kasar nan gaba da samar da abinci.
“Shugaban kasa ya bada wannan umarni dan samar da harkar noma da zata ja hankalin matasa dan su shiga cikin tsarin a dama dasu.
” saboda haka ina kira ga sauran gwamnoni jihohi cewa wannan wata koface da shugaban kasa ya bude dan samar da isassun gonakin noma.
“Wannan zai kawar da rashin aiki da matasa suke fama dashi da yin kasuwanci, kuma hakan zai samar da wada taccen abinci cikin kankanin lokaci”, a cewar sa.
A cewar sa shirin da shugaban kasa ya kaddamar a Daura matasa guda 1,500 suka shiga cikin harkar dan idonsu ya bude duba da sanya ido da gwamnatin Buhari take yi dan samar da abinci wada taccen abinci.