Tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Zaria.
Tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria Farfesa Ango Abdullahi, kuma daya daga cikin dattawan arewa, ya ce siyasa ce kawai da kuma bin umarnin Kasar Saudi Arebiya ya sa Shugaba Muhammad Buhari ya ki sakin Jagoran Ýan Shiá Ibraheem El-Zakzaky.
A hirar da ya yi da Jaridar Vanguard, ta ce Ýan Majalisar Tarayya, wadanda su ka zama hoto, sun ki taka rawar da ya dace na goyon bayan ka da a saki Malamin, duk kuwa da cewa suna wakiltar jamaá ne.
Farfesa Ango ya ce abin takaici ne sosai, yadda haka siddan Buhari ya ki sakin Alzakzaky, abin da ya sa mabiyansa ke ta zanga zangar da ya haifar da rasa rayuka da dukiyoyi.
‘’Kasar nan na fama da tashin-tashina iri iri, na makiya, da boko haram, da masu satar mutane. Yanzu kuma Buhari na so ya jawo mana abin da ya fi na Boko Haram tashin hankali’. In ji shi.
‘’Muna da dokokin kasa, wadanda su ka bayyana duk yadda za a tafiyar da komai. Ana nufin su Ýan Shi’a ba su da wata dama ce a cikin tsarin mulkin Najeriya?’Ya tambaya.
Farfesa Ango Abdullahi ya cigaba da cewa, ba Ýan Shiá ne kadai Buhari ya take wa hakkinsu ba. Hatta Sambo Dasuki, shi ma ya fada wannan komar ta Buhari.