Kirsimeti: Ku yi addu’a ga gwamnatin Tinubu ta yi nasara – Gwamnan Bauchi ga Kiristoci
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bukaci mabiya addinin Kirista da su yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu addu’a domin samun nasara.
Mohammed ya yi wannan roko ne a lokacin da al’ummar Kirista suka karbe shi a wani bangare na bikin Kirsimeti, ranar Litinin a Bauchi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Enugu Ta Sauya Shawarar Bude Gadar Da ta Ruguje
Ya ce nasarar da Shugaba Tinubu ya samu ita ma nasara ce a gwamnatinsa, yana mai jaddada cewa irin wannan addu’a ta dace don ganin shugabannin sun cika aikin da aka dora musu.
“Ku manta da jam’iyyun siyasa amma ku yi wa shugaban kasa addu’a a matsayin mutum kuma a matsayin shugaban kasa.
“Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), da sauran malaman addini su yi mana addu’a a matakai daban-daban na shugabanci.
“Ina rokon ku da ku yi wa Shugaba Tinubu addu’a domin idan bai yi nasara ba, hakan zai shafe mu.
“Ba batun jam’iyya ba ne, shi ne shugabanmu kuma ku ma ku yi mini addu’a saboda ni ne shugaban ku,” in ji shi.
Mohammed ya yi kira ga kowa da kowa da su yi addu’a ga hadin kan dukkanin jam’iyyun siyasa don ba su damar hada kai wajen inganta shugabanci nagari a jihar da kasa baki daya.
A wani labarin kuma:Rikicin Ribas: Tinubu ba zai dunkule hannu da kallo ba – Fadar Shugaban Kasa
Fadar shugaban kasa ta ce babu yadda za a yi shugaba Bola Tinubu ya yi shiru ya bar rikici ya barke a jihohi.
Hakan ya biyo bayan tsoma bakin da ya yi a rikicin siyasar Ondo da Ribas.
Masu lura da al’amura dai sun yi iƙirarin cewa abin da Tinubu ya yi na zagon ƙasa ga gwamnatin irin waɗannan jihohi ne.