Rikicin Ribas: Tinubu ba zai dunkule hannu da kallo ba – Fadar Shugaban Kasa
Fadar shugaban kasa ta ce babu yadda za a yi shugaba Bola Tinubu ya yi shiru ya bar rikici ya barke a jihohi.
Hakan ya biyo bayan tsoma bakin da ya yi a rikicin siyasar Ondo da Ribas.
Masu lura da al’amura dai sun yi iƙirarin cewa abin da Tinubu ya yi na zagon ƙasa ga gwamnatin irin waɗannan jihohi ne.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Enugu Ta Sauya Shawarar Bude Gadar Da ta Ruguje
Sai dai mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya yi imanin cewa an yi tafiya mai kyau.
Ngelale ya ce Tinubu zai ci gaba da tsoma baki a jihohin da ke fama da rikicin siyasa idan irin wannan ci gaban ya shafi kasar.
“Hakan ba shi da alaka da, ba shakka, ci gaban siyasa, tabarbarewar wani yanki ko jiha ko wata kasa da za ta iya rikidewa zuwa tada kayar baya,” in ji shi a gidan Talabijin na Channels, wani shiri da aka riga aka nada wanda ya ke fitowa a ranar Litinin.
“Idan Shugaban kasa ya ga haka, ba zai zauna a matsayin Babban Kwamandan Sojoji ya nade hannunsa ya yi shiru ba. Ina tsammanin abin da ya yi ke nan.
“Wato idan kai ne babban kwamandan rundunar soji kuma babban burinka shi ne tabbatar da cewa al’ummar Najeriya suna cikin koshin lafiya; cewa za su iya yin aiki a cikin wani yanayi mai natsuwa kuma ba sa sanya su cikin ko wace irin tabarbarewar tsaro, to ka sani idan rikicin siyasa ya shiga cikin wani abu da ke haifar da rashin tsaro na dan Adam, to akwai bukatar shugaban kasa ya shiga cikin lamarin kuma ya ya dauki wannan matakin da ya dace na shiga ciki,” in ji mai taimaka wa shugaban kasar