Zuwa 29 ga watan Afrilun 2020, cutar ta bulla a jihohi 34 na Nijeriya ciki harda Abuja. Inda jihohi biyu kawai suka rage a Nijeriya da cutar ba ta bulla ba, jihohin kuwa sune; jihar Ribas da kuma Kogi.
Cibiyar dake dakile cututtuka masu yaduwa, NCDC a ranar Laraba sun tabbatar da cewa an samu karin mutum 196 da suke dauke da cutar Korona a Nijeriya wanda wannan ya sanya adadin masu cutar yanzu a Nijeriya sun kai 1,728..
NCDC har wala yau sun ce mutum 11 sun sake mutuwa daga cutar, inda yanzu adadin ya kai 51 wadanda suka mutu.
The centre said that the breakdown of the 196 new infections recorded indicated that Lagos recorded 87 new cases and Kano, 24.
Cikin sabbin mutum 196 da aka samu dauke da cutar, 87 sun fito daga Legas ne, a yayin da aka samu 24 daga Kano. Sai kuma 18 daga Gombe, 17 a Kaduna, 16 a Abuja, sai 8 a Sakkwato, da kuma 7 daga Edo, sai 6 a Borno, sai kuma guda daya-daya a jihohin Yobe, Ebonyi, da kuma Adamawa.
NCDC sun ce ya zuwa karfe 11:55 na daren 29 ga watan Afrilu, mutum 1,728 ke dauke da cutar, a yayin da mutum 1, 370 ke ba su warke daga cutar ba. Inda mutum 307 suka warke daga cutar yayin da 51 suka mutu.