A yayin da ‘yan Nijeriya ke kokawa yanayin rayuwa, a lokacin ne suka wayi gari da labarin yunkurin karin harajin kayayyaki. A cikin makon nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin harajin kayayyaki a Nijeriya. Karin wanda shugaban kasar ya yi shi daga kashi 5 har zuwa kashi 7.
Ministar kudin kasar, Hajiya Zainab Ahmed, ta shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa an dauki matakin ne lokacin taron majalisar ministoci. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa; wannan sabon karin haraji ba zai soma aiki ba sai ya samu amincewar ‘yan majalisar dokokin kasar. Idan suka amince da sabon karin, to zai soma aiki a shekarar 2020.
Ta kara da cewa an kara harajin ne domin gwamnati ta samu damar iya biyan albashin da aka kara wa ma’aikata na dubu Talatin mafi karanci. A cewar ta, majalisar ministocin ta bukaci a tattauna da jihohi da kananan hukumomin kasar kan yadda za a tabbatar da karbar karin harajin kasancewa suna cikin masu morar sa.