Bayan da gwamnatin tarayya ta ba da izinin gina layin jirgin kasa na zamani daga garin Ibadan zuwa Kano akan kudi har dalar Amurka biliyan 5 da miliyan dari 3 ($5.3bn), al’ummar kasa musamman mazauna jihar Kano da Ibadan har sun fara tambayoyin koyaushe wannan aikin zai fara.
Idan mai karatu bai manta ba, Ministan Sufuri Mista Rotimi Amaechi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis inda ya shaida cewa a ranar Laraba ne gwamnatin tarayya ta amince.
Haka zalika ya bayyana cewa, sun nemi a ba su kudi domin fara aikin gina layin dogon daga garin Fatakwal zuwa Warri.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa; ba da jimawa ba aikin zai fara kankama kamar yadda gwamnatin tarayya ta tsara a karkashin ma’aikatar Sufurin.