Labari da suke fitowa da ɗumi-ɗuminsu daga birnin Manchester United na ƙasar Ingila na nuni da cewar babu tabbacin shahararren ɗan wasan gaban da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta saya wato Edison Cavani zai buga wasan da ƙungiyar zata fafata a ranar Asabar mai zuwa wato ƙarshen makonnan daza a shiga.
A ranar Asabar ɗin dai Manchester United zata kara wasanta da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle United, tunda dai aka fara fafata gasar ta ajin Firimiya ta bana kusan Manchester United tana ta samjn tangarɗa awasanninta musamman wasannin data fafata a filin wasanta na Old Trafford inda tasha kashi a hannun Crystal Palace dace 3 – 1 sannan kuma Tottenham ta ragargazata daci 6 – 1.
Dalinlin da yasa Edison Cavani bazai sami damar fafata wasan na ranar Asabar ba shine mafi yawan ‘yan wasan da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa suke saya bayan sunzo ƙungiyar sukanyi kwanaki 10 a killace domin tabbatar da cewar baya ɗauke da cutar ta Coronavirus domin gudun kada ya gogawa sauran ‘yan wasan daya taras a sabuwar ƙungiyar.
Ayanzu dai an tabbatar da cewar Edison Cavani zai kwashe kwanaki 10 a killace a birnin na Manchester kafin ya fara fafata wasa, wannan kwanaki goma da zai kwashe shine yasa bazai sami damar buga wasan na ranar Asabar ba da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Manchester United zata kara da Newcastle United.
Wannan cuta ta Covid 19 har yanzu ganaci gaba da rugurguzar mutane a nahiyar turai inda koda a wannan makon ta kama ‘yan wasa da dama daga cikin ‘yan wasan data kama harda shahararren ɗan wasannan wato Christino Ronaldo.