Kocin kungiyar kwallon kafa ta PSG,Christopher Galtier na fuskantar daurin shekaru 3 da kuma tarar Yuro 45,000 idan aka same shi da laifin cin zarafin musulunci
A lokacin da yake aikin horar da yan wasan OGC Nice ya taba tura sakon kar takwana ga wata kungiyar dake buga gasar Ligue 1 ta kasar Faransa
Inda yake cewa kun hada yan wasanku kowa da dogon gemu ,bakake yan Afirika kuma kusan rabinsu suna zuwa Masallaci a ranar Juma’a
Abinda ka iya zama kalaman nuna wariyar launin fata da kuma kalaman batanci akan addinin musulunci
Idan har aka samu Galtier da laifin kalaman wariyar launin fata zaa iya daure shi a gidan gyaran hali dake Faransa da kuma cinsa tarar yuro 45,000
Jaridar Dailypostngta ta bayyana Cewar Galtier shi da dansa John Vlalovic Galtier zasu hallara kotu ranar Juma’a domin amsa wasu tambayoyin da zasu nuna ko yana da laifi ko kuma babu
Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain na gab da sallamar kocin na kasar Faransa bayan da kungiyar ta kasa tabuka abin azo agani a kakar wasa ta bana
KARANTA NANIna so ku rugurguza dukkanin inda yan bindiga suke – Shugaban Soji ga Jami’ai
Duk da lashe gasar Ligue 1,PSG na bukatar nemo wani koci da zai iya kai kungiyar ga nasarar lashe kofin Uefa Champions League
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da kuma tawagar yan kwallon kafa ta kasar Sifaniya Luis Enrique na gab da zama sabon kocin kungiyar
Kasar Faransa na kokarin hukunta duk wani wanda aka samu da laifin nuna wariyar launin fata ganin cewar akwai yan wasa da yawa daga Afirika da suke taka leda a Faransar
A WANI LABARIN KUMABana Bukatar Kujerar Minista-Tsohon Gwamna
Tsohon Gwamnan Jahar Benue Samuel Ortom ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da abinda ya kira bayanan Karya da ake yadawa a kafafen watsa Labarai
Na cewar wai yana kamun kafa ga sabuwar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu domin a yi masa kujerar Minista,inda yace ko kusa baya tunanin a bashi wani Mukami