Shettima Ya Ziyarci Sultan, Ya Nemi Goyon Bayan Arewa Ga Gwamnatin Tinubu A Harkar Tsaro
A ranar Alhamis ne mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci shugabannin arewa da su marawa kokarin gwamnatin Bola Tinubu wajen tunkarar kalubalen tsaron Najeriya.
Shettima ya yi wannan kiran ne a Sokoto a lokacin da ya kai wa Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku gaisuwar Sallah a fadarsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina so ku rugurguza dukkanin inda yan bindiga suke – Shugaban Soji ga Jami’ai
“Ina kira ga shugabannin siyasar mu da su hada kai don tunkarar kalubalen da suka hada da rashin tsaro, talauci da rashin ci gaba a yankin,” in ji Shettima a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Olusola Abiola ya fitar.
“Shugaba Tinubu yana sane da kalubalen da mutanen mu ke fuskanta – matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin Arewa maso Yamma kuma yana daukar matakai masu nisa don magance lamarin.”
Yayin da yake mika sakon taya murna ga shugaba Tinubu, mataimakin shugaban kasar ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da hadin kai, inda ya bayyana cewa “ba za a taba samun zaman lafiya ba tare da ci gaba ba, ba za a taba samun ci gaba ba tare da zaman lafiya ba.”
Ya ce gwamnati mai ci ta yarda da rawar da Sarakunan gargajiya ke bayarwa.
Mataimakin shugaban kasan ya kuma dorawa gwamnan jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu Sokoto alhakin samar da jagoranci mai ma’ana tare da yi masa gargadi da ya ci gaba da kulla kyakkyawar alaka da shugabanni a fadin jihar.
Da yake jawabi tun da farko a wajen wata ‘yar gajeriyar liyafar da aka yi wa mataimakin shugaban kasa a gidan gwamnati, Sakkwato ya nuna jin dadinsa da ziyarar, inda ya bayyana wannan karimcin da mataimakin shugaban kasar ya yi a matsayin nuna tsananin kaunar jihar Sakkwato da al’ummarta.
A nasa bangaren, Sarkin Musulmi ya godewa Shettima bisa wannan karramawar da aka yi masa na Sallah tare da neman hikima da karfin Allah ya sauke nauyin da aka dora masa a matsayin dan kasa na biyu.
A wani labarin kuma:Ina so ku rugurguza dukkanin inda yan bindiga suke – Shugaban Soji ga Jami’ai
Shugaban Rundunar Sojojin Sama (CAS), Air Vice Marshal (AVM) Hassan Bala Abubakar, ya tuhumi jami’an sojin sama da su tabbatar da cewa an rugurguza masu aikata laifuka ko kuma a tilasta musu mika wuya.
Ya bayar da wannan umarni ne a lokacin da yake cin abinci tare da dakarun Operation Hadarin Daji a Katsina domin gudanar da bukukuwan Sallah na bana da nufin kara musu kwarin gwiwa.