Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce kofar Jam’iyyar su ta NNPP a bude take ga kowa, ko da kuwa a baya kun taba samun sabani da shi.
Kwankwaso wanda kuma shine jagoran jam’iyyar NNPP na wannan jawabi ne yayin da ake tsaka da tattaunawa da wasu kusoshin APC da suke burin sauya sheka zuwa jam’iyyar sa.
Daga cikin wadanda ake tattaunawa da su domin ganin sun koma ita wannan jam’iyyar har da Sanatan Kano ta tsakiya mai ci Ibrahim Shekarau, da sauran su.
Kafin haka dama tuni tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Alhassan Rurum ya ajiye shahadar APC tare da Hon. abdurrahman Kawu Sumaila, kuma suke shirye shiryen komawa NNPP.
Yayin wata hira da aka yi da shi da wata radiyo a Kano, Kwankwaso ya ce jam’iyyar su na bukatar karin mabiya, kuma duk wanda yake da sha’awar shiga kofar su a bude take.
Ya kuma ce tsagin Sanata Shekarau da akewa lakabi da G7, suma damar a bude take a wajen su, bayan da suka gaza samun abinda suke so a jam’iyyar APC.