Farfesa Maryam Aminu, Farfesa a sashen koyar da ilimin sanin kananan halittu da ido da na iya gani a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, ta ja hankalin masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi akan su sa hankali a daidai lokacin da aka bude makarantun Sakandare domin ci gaba da gudanar da ayyukan, inda ta jaddada cewa; tabbas cutar korona gaskiya ce.
Farfesa Maryam ta bayyana hakan ne a yayin da take gabatar da jawabi a karkashin jawaban da kungiyar ‘Fulbrigth Alumi Association of Nigeria’ suka shirya akan cutar korona.
Farfesa Maryam ta ce a duk duniya ana da mutum akalla miliyan sha shida da suka kamu da cutar korona, inda akalla mutum dubu dari shida da dubu arba’in suka rasa rayukansu. A don haka ta ce idan aka yi la’akari da yadda ake samun masu korona a Nijeriya duk da karancin gwaji, ya nuna cewa akwai cutar a kasar.
Ta ja hankali akan muhimmancin bin matakan kariya domin kare kai daga kamuwa da cutar, wanda ya hada da sanya takunkumin fuska, bada tazara, wanke hannu a kai, a kai da sauran su.
Wadannan abubuwa suna da matukar muhimmanci ya zama ana yinsu kafin a kai ga komawa makaranta.