Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce akwai yiwuwar ya kulle jihar Ribas baki daya a watan Janairu domin ganin ya dakile yaduwar korona da ta dawo a karo na biyu.
Gwamnan wanda yake yi wa wadansu jama’a bayani a ranar Lahadi a garin Ikwerre, ya ce matakin ya zama wajibi ne sakamakon rashin bin ka’idodin dakile yaduwar cutar da wasu ba su yi a jihar.
Gwamnan har wala yau ya yi barazanar kulle wuraren ibada idan har suka daina sanya takunkumin fuska da sauran bin hanyoyin kariya daga korona.