Daga Wakilinmu Da BBC Hausa
Annobar Cutar korona ta hana Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, zuwa ɗaurin auren ɗansa Hamisu.
Bayanin hakan ya fito ne a wata sanarwa da Kakakin rundunar sojin ƙasa, Kanal Sagir Musa ya fitar, sanarwar ta ce sakamakon ƙara yaɗuwar cutar korona da ake samu, Janar Buratai ba zai samu damar halarta ko karɓar baƙi ba a yayin ɗaurin auren da za a gudanar a yau Juma’a ba.
A ranar Alhamis bayanai sun nuna cewa cutar koronar ta yi ajalin babban jami’inta da ke kula da runduna ta shida da ke birnin Fatakwal na jihar Ribas wanda ke halartar wani taro na sojojin ƙasar.
A yanzu dai duk sojojin da suka halarci taron da shi kansa Janar Buratai ɗin za su killace kansu kuma ba za su halarci ɗaurin auren ba.