An sake samun mutum takwas da cutar korona ta kashe a Nijeriya, lamarin da ya sanya yanzu jimillar wadanda cutar ta kashe a Nijeriya sun kai 1, 761 kamar yadda alƙalumman Hukumar da ke daƙile cutuka masu yaɗuwa na Nijeriya, NCDC ya nuna.
Alƙalumman kuma sun ce an sake samun mutum 574 da suka kamu da cutar. Inda a Kwara aka samu mutum 98 sai Lagos- 81, Edo- 59, Ondo- 44, FCT- 41, Kano- 34, Ogun- 33, Kaduna- 29, Osun- 28, Enugu- 23, Rivers- 18, Delta-16, Akwa Ibom-15, Bauchi-12, Imo-10, Borno-8, Niger-8, Kebbi-7, Nasarawa-5, Gombe-3, sai Ekiti-2
Adadin wadanda cutar ta cafke a Nijeriya sun kai 146,928 a yayin tuni aka sallami mutum 123,009.