Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a manna takardar sammacin karar da PDP ta shigar a ofishin Yakubu Dogara da ke majalisar wakilai.
A ranar Talata ne alkalin kotun, Okon Abang, ya saka ranar 5 ga watan Fabarairu domin bayyanar Dogara a gabansa.
Sai dai, masu kara; kungiyar UGRPO, sun yi zargin cewa Dogara ya dakile duk wani yunkuri na damka masa sammacin kotu.
Duk da lauyan Dogara ya garzaya zuwa kotu wurin Jastis Abang domin karbar sammacin, Alkalin ya ce zai fi kyautuwa a lika takardar a ofishin Dogara.
Kungiyar UGRPO, a ranar Talata, ta shigar da sabuwar karar neman kotu ta tsige Dogara bayan wacce jam’iyyar PDP ta shigar, kamar yadd Premiumtimes ta rawaito.
A dukkanin karar, masu kara sun roki kotu ta tsige Dogara saboda ya sauya sheka zuwa APC bayan samun nasararsa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan PDP, Mista Jubril, ya roki kotu ta daga kafa wajen sauraron karar saboda har yanzu Dogara yana sharbar romon zaman mamba a majalisa da tikitin jam’iyyarsu.
Masu Kara; PDP da shugabanta na jihar Bauchi, Hamza Koshe Akuyam, sun bukaci Dogara ya bar kujerarsa bisa dogaro da sashe na 68(1) na kundin tsarin mulki, kamar yadda Channels ta rawaito.
A cewarsa, doka ta bukaci dan majalisa ya sauka daga kujerarsa matukar ya sauya sheka zuwa wata jam’iyyar daban ba tare da jam’iyyarsa na fuskantar wani rikici ba.
A cewarsu, bai kamata ko kadan Dogara ya cigaba da zama a zauren majalisa da nasarar da ya samu da sunan PDP ba.