Wata Kotu ta Makurdi Upper Area 2, a ranar Litinin ta bayar da belin Sewuese Angum, wacce ake zargi da barazanar za ta kashe makwabciyarta, Mercy Ashema a cikin kwana uku.
Da take yanke hukunci, Alkalin kotun, Misis Rose Iorshe, ta ce za ta bayar da belin wanda ake tuhuma ne a kan kudi Naira 50,000 da kuma wanda zai tsaya mata.
Mai gabatar da kara daga ‘yan sanda, Insfekta Veronica Shaagee, ta fadawa kotun cewa Ashema ce ta shigar da karar a ofishin ‘yan sanda na D, Unguwar Ankpa a Makurdi a ranar 25 ga watan Agusta.
“A daidai wannan ranar, da misalin karfe 3:30 na yamma, lokacin da ita (Ashema) ta dawo daga aiki, tana bude kofar gidan daga dawowarta, makwabciyarta Sewuese Angum mai adireshi daya, ta zuba yashi a jikinta kuma ta sha alwashin cewa cikin kwanaki uku za ta mutu.
Shaagee ta ce suna ci gaba da bincike a don haka a ba su karin lokacin domin kammala binciken.
Ta ce wanda ake tuhuma laifin na ta ya saba wa sashi na 397 da 263 na dokoki kamar yadda doka ta tanada.
Wacce ake zargi ta musanta aikata laifin.
Alkalin kotun ya dage sauraron karar har zuwa ranar 16 ga watan Satumba, domin ci gaba da sauraren karar.