An sake dage zaben ‘yan majalisar dokokin Somaliya har zuwa karshen watan Nuwamba, matakin dai zai jinkirta zaben shugaban kasa a kaikaice.
A makon nan ne ya kamata a kammala kada kuri’un ‘yan majalisar, inda za a gudanar da zaben kakakin majalisa da rantsar da ‘yan majalisar a mako mai zuwa-a lokacin ne za su zabi shugaban kasa a ranar 10 ga watan Oktoba.
Amma hukumar gudanar da zaben ta fitar da sabon jadawalin zaben wanda ke nuni da cewa za a zabi ‘yan majalisar ne a tsakanin 1 ga Oktoba zuwa 20 ga Nuwamba.
Jadawalin, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ta gani, bai bayar da ranar da ‘yan majalisar za su zabi shugaban kasa ba.
Wa’adin gwamnatin na yanzu ya kare ne a watan Fabrairu.
Jinkirin gudanar da zaben, da kuma takaddama kan yunkurin shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed na kokarin tsawaita mulkinsa, ya haifar da rikicin siyasa da tashin hankali a kan titunan babban birnin kasar.