Wata babbar kotu da ke zaune a Asaba, babban birnin jihar Delta, ta dakatar da taron karamar hukuma na jam’iyyar APC Mai Mulki, Wanda da aka shirya Gudanarwa a ranar 4 ga Oktoba, shekarar 2021.
Kazalika rahotannin da majiyar jaridar Dimokuradiyya kesamu na nuna cewa,, kotun ta kuma hana Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ai’yana kan shi a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APCn har sai an yanke hukunci a nan gaba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa a jiya
A gefe guda jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Olorogun Elvis Ayomanor, wanda ya jagoranci wasu jami’an jam’iyyar APC na Delta, ya garzaya kotu, biyo bayan babban taron mazabu na ranar 10 ga watan Yuli, 2021, wanda ake zargin an janye.
A wani labarin Kuma na daban
Da dumi duminsa: Zamfara ta sanya Dokar tabaci, tare da kulle Makarantu
Daga Wakilin Dimokradiyya Usman Salisu Gurbin Mikiya
Gwamnatin Jahar Zamfara ta sanya dokar tabaci daga safe zuwa dare a Kananan Hukumomi guda 14 a Jahar.
Gwamnatin ta kuma kulle dukkanin Makarantun Gwamnati dana Yan Kasuwa, dake a Kananan Hukumomi guda 14 na Jahar.
Matakin ya biyo bayan shiga garin Kaya a Karamar Hukumar Maradun ta Jahar da Yan bindiga dadi suka yi, inda suka sace Dalibai da ba’a San konawa bane, a Makarantar Sakandire ta Jeka ka dawo ta Kaya, a Karamar Hukumar Maradun ta Jahar Zamfara, inda ya Kasance Mahaifar Gwamna Bello Matawalle.
Kamar yadda Dan Asalin Garin ya bayyana Abu Kaya, yace Makarantar, nada yawan Dalibai 300, sun kuma shiga Makarantar da Misalin Karfe 11:00 ta Safe a ranar Laraba a lokacin da ake tsaka da karatu.
Acewar Gidan Talabijin na TVC, Dokar tabacin zata fara daga karfe 8 na yamma zuwa karfe bakwai na safe.
Wannan matakin kamar yadda Mahukunta suka bayyana, an dauke shi ne domin shawo kan Matsalar Yan bindiga dadi, da Garkuwa da mutane a Jahar.