Kotu ta kori karar da ke neman dakatar da gudanar da zabe, jarrabawa a ranar Asabar
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da Ugochukwu Uchenwa dan cocin Seventh-day Adventist ya shigar yana neman a dakatar da gudanar da zabe da jarrabawa a ranar Asabar.
Da yake yanke hukunci kan karar a ranar Laraba, Mai shari’a James Omotosho ya ce karar ba ta da tushe, bata da wani amfani.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ƴan sanda sun cafke mutane 3 da ake zargi da yunkurin yin garkuwa da mutane a Bauchi
Ugochukwu, wani dattijon cocin ya shaidawa kotu a cikin kararsa cewa ranar Asabar ce ranar ibada da tsayar da jarrabawa da zabe a ranar tauye hakkinsa da sauran mabiya cocin ne.
Mai shigar da karar ya roki kotun da ta bayar da umarnin haramtawa gwamnatin tarayya ci gaba da gudanar da zabe da jarrabawa a ranar Asabar domin a daina tauye hakkinsu na ibada.
Mai shari’a Omotosho, a cikin hukuncin da ya yanke, ya bayyana cewa muhimman hakkokin da mai gabatar da kara ke nema ba zasu yiwu ba, kuma manufar gwamnati za ta iya tauye su.
Bugu da kari, alkalin ya ce cocin Seventh-day Adventist na cikin tsiraru ne a Najeriya kuma ba za a iya dora koyarwarsa a kan yawancin mabiya addinai a kasar ba.
Da yake magana da manema labarai bayan yanke hukuncin, lauyan wanda ya shigar da karar, Benjamin Ahaemefule ya ce wanda yake karewa ya garzaya kotun daukaka kara domin kara gwada sa’a.
Mista Ahaemefule ya ce duk da cewa wanda yake karewa ya samu nasara a wasu bangarori na karar, sun yi rashin nasara a babbar karar don haka akwai bukatar a tunkari kotun daukaka kara.
“Kotu ta amince da mu cewa tana da hurumin sauraren karar mu.
“Kotun ta kuma amince da mu cewa dattijo Uchenwa yana da hurumin kafa wannan mataki domin tabbatar da hakkinsa da na daukacin mambobin cocin Seventh-day Adventist Church Nigeria.
“Kotu ta amince da mu cewa ana tauye hakkin masu sha’awar sha’awa.”
“Kotun, duk da haka, ta ki aiwatar da ‘yancinmu tana mai cewa masu ra’ayin addini tsiraru ne ba masu rinjaye ba.
A wani labarin kuma:Ƴan Sanda sun kama sojan gonar da ke da hannu kan fashi da makami a Kaduna
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wani sojan bogi da ake zargin yana da hannu wajen fashi da makami.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Kaduna.