Kotu ta hana Murja Kunya amfani da kafafen sada zumunta
Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Nasiru Saminu a ranar Litinin ta bayar da belin Murja Kunya a kan kudi naira 500,000.
Ƴar TikTok ɗin dai ta nemi a bayar da belinta ne, biyo bayan umarnin da kotun shari’ar Musulunci ta Kano ta bayar na cewa wani likitan tabin hankali ya duba lafiyarta.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ƴan Sanda sun kama sojan gonar da ke da hannu kan fashi da makami a Kaduna
A hukuncin da ya yanke a ranar Litinin, Mai shari’a Saminu ya ce sharuddan belin sun hada da wasu mutane biyu da za su tsaya mata, wadanda suka hada da wani dan uwa da wani mutum mai mallakar fili a karamar hukumar Kano.
Alkalin kotun ya hana Kunya amfani da shafukan sada zumunta har sai an yanke hukunci.
Alkalin kotun ya ce “Duk wani keta dokar da aka yi zai tilastawa Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya kama tare da dawo da ƴar TikTok ɗin a gaban kotu.”
Alkalin ya kuma bayar da umarnin cewa, “Lauyoyin wadanda ake kara, Babban Lauyan Gwamnati, Wakilai daga Hukumar Hisbah, da Kwamishinan ‘Yan Sanda dole ne su hallara domin magance gyaran dokar da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi wa dokar da aka yi wa kwaskwarima domin yanke hukunci mai kyau.”
Don haka kotun ta dage zaman har zuwa ranar 16 ga Mayu, 2024, domin ci gaba da shari’a
A wani labarin kuma:Kotu ta kori karar da ke neman dakatar da gudanar da zabe, jarrabawa a ranar Asabar
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da Ugochukwu Uchenwa dan cocin Seventh-day Adventist ya shigar yana neman a dakatar da gudanar da zabe da jarrabawa a ranar Asabar.
Da yake yanke hukunci kan karar a ranar Laraba, Mai shari’a James Omotosho ya ce karar ba ta da tushe, bata da wani amfani.