Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamnan Kaduna
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna a jihar Kaduna ta tabbatar da nasarar Gwamna Sani Uba.
Da take yanke hukunci a cikin karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru, suka shigar domin kalubalantar nasarar Gwamna Uba Sani, kwamitin ya ce Sani ya yi daidai.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yajin Aiki: Kar ku yi watsi da umarnin kotu – AGF ya gargadi NLC, TUC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Sani wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.
Amma Ashiru da jam’iyyarsa sun ki amincewa da sakamakon inda suka nufi kotun gaba.
Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a Victor Oviawe ya yanke hukunci ta hanyar Zoom ranar Alhamis
A wani labarin kuma:Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta kori Gwamna Uba Sani, ta bayyana cewa zaben Kaduna bai kammalu ba
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna da ke zamanta a jihar Kaduna a ranar Alhamis ta kori Gwamna Uba Sani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga kujerarsa.
Kotun ta bayyana cewa zaben gwamna na 2023 a jihar bai kammala ba.